Kotu Taci Tarar Gidan Rediyo Da Talabijin Na Gotel Mallakar Atiku Abubakar Bayan an kwashe shekaru 6 da Kabiru Arayu ya shigar da kara yana neman gidan rediyo da telibijan Gotel mallakar tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar a biyashi hakkinsa, A ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni kotu ta yanke hukunci inda ta tabbatar masa da abun da ya nema.

Babbar kotun jihar Adamawa ta yanke hukuncin gidan radiyo da talabijan na Gotel da ke Yola fadar jihar, ya biya tsohon ma’aikacinsa dan jarida Kabiru Arayu diyyar naira miljyan 6.1 na karar da ya shigar na ci-da-guminsa.

Da ta ke yanke hukunci, mai shari’a Helen Nuhu Hammanjoda ta ce kotu ta dauki wannan matsayin ne saboda kin biyan dan jaridan hakkinsa na aikin kwangilar da yayi, kotu ta ce ya sabawa sashi na 167 karamin sashi na daya na dokar kasa.

Wannan hukunci na kotu na zuwa ne a lokacin da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya ke kokawa da ci-da-gumin ‘ya’yanta inda kafofin yada labarai da jaridu ke daukan ‘yan jarida ba tare da biyansu albashi ko alawus-alawus ba.

Yayin da lauya mai kare dan jaridan Barrister Francis Ngaro ke sam barka da yadda shari’ar ta kaya, lauya mai kare gidan radiyo da telabijan na Gotel Ibrahim Gwary ya ce suna duba yiwuwar daukaka kara.

Tun farko, dan jarida Kabiru Arayu ya shigar da kara yana neman diyyar naira miliyan 20 da tara kamin hukunci da kotu ta bayar na a biya shi naira 6.1 a shari’ar da ta dau tsawon sama da shekaru 5.

You may also like