Kotun tabbatar da da’ar ma’aikata ta kori karar da akewa shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki,kan zargin da ake masa nayin karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka.
Tun a ranar 4 ga watan Mayu ne Saraki ya nemi kotun da tayi watsi da tuhumar da ake masa bayan da masu gabatar da kara suka rufe gabatar da hujjojinsu.
A hukuncin kotun na yau Alkalin kotun,Danladi Umar yace masu gabatar da kara sun gaza wajen gamsar da kotu zarge zargen da akewa Saraki.