Kotun daukaka kara ta tabbatar da takarar Uba Sani







Kotun daukaka kara dake Abuja ta tabbatar da Sanata Uba Sani a matsayin dantakarar gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyar APC a zaben 2023.

Sani wanda a yanzu shi ne sanata dake wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya ya samu tikitin takara ta hanyar sulhu.

Rashin gamsuwa da yadda aka fitar da dantakarar ne ya sa, Sani Sha’aban daya daga cikin masu takara ya garzaya kotu inda yake kalubalantar nasarar da Uba Sani ya samu.

A cewar sa an gudanar da zaben ne ba tare da wakilai masu kada kuri’a ba.

Amma kuma kotun tarayya dake Kaduna tayi watsi da karar inda ta ce bata da hurumin sauraron shari’ar.

Hakan ya sa ya daukaka kara ya zuwa kotun daukaka kara dake Abuja inda ita ma tayi da karar.






Previous article2023: Tinubu will win with landslide in South West, APC claims




Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like