Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Gwamnan Jihar EdoKotun daukaka kara dake zamanta a Benin, babban birnin jihar Edo ta tabbatar da nasarar da gwamnan jihar Godwin Obasaki,na jam’iyar APC, ya samu a zaben da aka gudanar cikin watan Satumbar shekarar 2016.

Ize Iyamu,dan takarar jam’iyar PDP, ne ya shigar da kara gaban kotun yana kalubalantar nasarar da Obasaki ya samu a zaben. 

 Da take yanke hukuncin shugabar rukunin alkalan da suka saurari shariar, Monica Dongba Mensen, tace  wadanda suka daukaka karar basu da gamsassun hujjoji, saboda haka kotu bazata iya soke zaben ba kan zargin cewa alkalan kotun baza su iya gudanar da aikinsu yadda yakamata ba. 

Dongba Mensen ta kuma yi watsi da ikirarin da jam’iyar PDP da dantakararta sukayi na cewa ba abasu cikakken lokaci ba domin su sake kidaya kuri’un  da aka kada musu, wanda ya zarce kwanaki goma sha hudu da doka ta bayar.

Saboda haka kotu tayi watsi da daukaka karar Ize Iyamu. 

You may also like