
Kotun koli ta dakatar da Babban Bankin Najeriya CBN daga shirin sa na daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin Naira a ranar 10 ga watan Faburairu kamar yadda bankin ya tsara.
Jihohin Kaduna da Zamfara da kuma Kogi su ne suka shigar da kara gaban kotu.
A yayin zamanta na yau kotun ta bayar da umarnin wucin gadi har zuwa ranar 15 ga wata lokacin da za ta cigaba da sauraron karar.