Kotun Soja Ta Ragewa Wani Soja Mukami  


Wata kotun soja ta musamman a ranar Alhamis ta ragewa Ibrahim Sani, mukami daga Manjo Janar zuwa Birgediya Janar.

James Gbum, shugaban kotun  shi ya ragewa Sani mukami bayan ya same shi da aikata laifi biyar dake da alaka da cuta. 

Sani ya dade yana fuskantar shari’a  a gaban kotun tun shekarar 2015 lokacin da aka zarge shi da laifin sayarwa da kuma mallakawa kansa wasu filaye mallakar rundunar.

 Kotun tayi zamanta a barikin Mogadishu dake Asokoro Abuja. 

Gbum, ya kuma umarci  mai laifin kan ya dawo da miliyan 26 na kudin da ya samu bayan ya sayarwa da kansa filin. 

Kotun tace Sani ya mallakawa kansa filin mai girman hekta 436, a Abuja, kana ya sayar da filin.  

Shugaban kotun yace sani ya wuce umarnin da aka bashi nayiwa filin takardar mallaka  da ga hukumomin dake kula da kasa a birnin tarayya.

Yace mai laifin ya raba filin inda yayi amfani da wani kamfani na karya,wanda shi kadai ne ma mallakinsa. 

Gbum yace mai laifin ya siyar da wani bangare na filin ga mutane uku kan kudi naira miliyan 10, miliyan 7 da kuma miliyan 6.

Amma shugaban kotun yace, hukuncin bazai tabbata ba har sai hukumar koli ta soji.

Paul Sule,shine lauyan Sani ya kuma ce zai roki hukumar koli ta jingine hukuncin.

You may also like