Kowa Na Da Hakkin Duban WataAkan haka ne shugabannin al’umma da na addini ke jan hankulan jama’a akan tanadin shari’a dangane da ganin wata.

Samun ganin jinjirin wata, ranar 29 ga watan Sha’aban shekarar Musulunci ko kuma cikarsa kwana 30, shi ne sharadin soma azumin watan Ramadan ga Musulmin duniya.

Sai dai wasu lokuta a Najeriya wasu Musulmi kan samu rabuwar kawuna dangane da ganin wata, duk da yake kwamitin duban wata na kasa da na fadar shugaban majalisar koli akan lamurran addinin Musulunci, na kokarin sanar da jama’a kwanakin watannin Musulunci.

Shugaban Majalisar kuma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci jama’a su daina kula da batun kwanan watan wasu kasashe irin Saudiyya, su mayar da hankali ga umurnin da shugabanninsu suka basu.

Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III

Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar III

Batun dubawa da tabbatar da ganin watan Musulunci nauyi ne da ya rataya a wuyar jagoran Musulmi, saboda haka shugaban kwamitin kula da lamurran addinin Musulunci a fadar Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne Wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya ce a Najeriya Sarkin Musulmi ne shari’a ta dorawa wannan nauyin.

Kuma acewar sa Sarkin Musulmi yana aiki tare da Sarakuna da uwayen kasa, da Malaman addini kafin yin matsaya akan ganin wata.

Malaman addinin Musulunci na ci gaba da tsokaci akan batun dubawa da tabbatar da ganin wata, da kuma ko ganin wata a wata kasa yana isarwa jama’ar wata kasa?

Sarkin Malaman Sakoto Malan Yahaya na Malam Boyi ya ce akwai sabanin malamai a kan batun, amma da yawan malamai sun tafi akan hadisin da ke cewa idan an ga wata a dauki azumi kuma a ajiye idan an ga wata.

Malamin ya ce wannan magana ce mai nufin idan an ga wata wani wuri ya isarwa dukan musulmi na ko’ina.

Shi kuwa Alkalin Malaman Sakoto Malam Ahmad Helele ya ce ba laifi yin amfani da ganin watan kasar Saudiyya, inda ya kafa hujjoji da ayoyin alkur’ani.

Lokacin Ramadan lokaci ne da ake karfafa gwiwar Musulmi du dage da ibadah tare da aikata ayyukkan alkhairi.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like