Kowa ya tuna bara, bai ji dadin bana ba


580b21224379a

 

Yan kasar Libya na ci gaba da kukan bakin ciki game da rashin tsohon shugabansu marigayi Muhammad Gaddafi,sakamakon irin halin ha’ula’i da suka fada a ciki a yau.

Bayan shekarar 5 kacal da mutuwar Kaddafi,al’umomin kasar Libiya suka fara kewar rayuwar raha da walwala da suke ciki a da.

Wannan nadamar dai ta biyo bayan irin matsannancin halin rayuwa,rashin kwanciyar hankali da wadata,tashe-tsahen hankula da suka jibanci kabilanci da ta’addanci,karamcin cimaka,ruwan sha da na wutan lantarki da suka dabaibaye Libya,tun bayan gushewar mulkin tsohon shugaban kasar wanda ya share shekaru 42 yana kan karagar mulki.

Wata ‘yar kasar Libiya mai suna Faiza Al Naas ta ce : “A yau,muna bakin cikin rashin Muhammad Kaddafi,duk da yake ina kunyar furta wadannan kalaman.Ganin irin yadda dubban matasa suka sadaukar da rayuwarsu a wajen ganin bayansa”.

A yanzu haka,kasar Libiya wadda a baya ta kasance tamkar wata aljanna a doron duniya sakamakon irin arzikin man fetur da take shi,ta zama wata mafakar miyagu inda manyan-manyan masu safarar mutane da miyagun kwayoyi tare da kunyoyin ta’adda kamar su Daesh suke cin karensu ba babbaka.

You may also like