Kowacce Rana Osinbajo Yana Magana Da Buhari – Lai Muhammad 


Hakkin mallakar Hoto:Channels Tv

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad yace mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo, kullum sai ya gana da shugaban kasa Muhammad Buhari,inda yace akwai yarda mai karfi a tsakanin mutanen biyu. 

Muhammad ya bayyana haka ne a tattaunawar da yayi da gidan talabijn na Channels a shirinsu na siyasa.

Da aka tambayeshi ko Buhari yana goyon bayan ganawar da Osinbajo yake da shugabannin Arewa da kuma na yankin kudu maso gabashin kasarnan   ministan yace babu abin damuwa akan wannan.

“mukaddashin Shugaban kullum sai yayi magana da shugaban kasa  saboda haka ina da yakinin cewa shugaban kasar yana sane da dukkanin abinda ke faruwa, lallai akwai yarda sosai tsakanin mutanen biyu bana tunanin akwai abin damuwa a kan wannan batu, “yace.

Lai yakara da cewa yanzu gwamnati ta maida hankali kan farfado da tattalin arzikin kasarnan da kuma dora kasar a turba mai kyau.  

You may also like