Kuɗin Da Aka Gano A Legas Na Yaƙin Neman Zaɓen Jonathan Ne – Ibrahim Ibrahim Tsohon Mataimakin Darakta a hukumar leƙen asiri ta ƙasa, Ibrahim Ibrahim ya  yi ikirarin cewa Dala milyan 24 da aka gano a wani gidan alfarma a Legas, an ware su ne don yakin neman zaben Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan a shekarar 2015.

Ya ƙara cewa duk da yake a wancan lokacin an ba Shugaban hukumar, Oke Ayo umarnin raba kuɗaɗen  ga wasu jigogin jam’iyyar PDP amma kuma bai san dalilin da ya sa ya ki bin umarnin ba. A cewarsa, an yi amfani da hukumomin tsaro wajen karkatar da kuɗaɗen don gudanar da yaƙin neman zaɓe amma ana rabewa da harkar tsaro.

You may also like