Ku Bawa Kanawa Aiki Su Daina Daba – Rundunar Yan Sandan Jihar KanoKakakin rundunar ‘Yansandan jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya, ya bukaci kwamashinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba da Kwamashinan kananan hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo da su hada hannu wajen taimakawa matasa da ayyukan yi domin raguwar ‘yan daba da masu shaye shayen miyagun kwayoyi a ciki da wajen jihar Kano baki daya.

DSP Majiya yana wannan kiran ne ta cikin shirin Dansanda Abokin Kowa da aka gabatar da yammacin jiya lahadi ta makon da ya gabata a gidan Rediyo Freedom.

Ya kara da cewa yin hakan zai taimakawa matasan da suka tuba suka daina harkar daba da kwacen wayoyi wanda ba zai sa su koma gidan jiya ba wanda ba fatan hakan ake ba, kuma zaman lafiya da tsaro zai cigaba da dorewa a fadin jihar baki daya.

You may also like