Kungiyar gwadago ta kasa NLC ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano ta hanzar kamala biyan albashin ma’aikata na watan Disambar daya gabata, da kuma na ‘yan fansho a jihar.
Shugaban kungiyar reshen Kano Kwamared Kabiru Ado Munjibir ne ya yi wannan kiran jim kadan bayan kamalla ziyara musamman a wasu kamfanoni biyar mallakin wani mutumin kasar China Mr Lee domin ganin ma’aikatan kamfanin sun sami yancin kafa kungiya.