Ku Nemin Shawara Da Taimakon Kwararru Don Fidda Kasar Nan Daga Kangi-Sarkin Kano


images-5

 

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga gwamnatin tarayya bisa jagoranci Muhammadu Buhari da ta nemi shawara da taimakon kwararru akan ilimin tattalin arziki don fitar da kasar daga halin da ta fada na tabarbarewar tattalin arziki.

Sarkin na Kano ya yi wannan batu ne a jiya Laraba a fadar gwamnatin Kano a yayin da ya kai ziyarar nan ta al’ada da sarki ke kai wa gwamna a duk ranar hawan Nasarawa.

Sarkin ya ce kwararru za su taimaka matuka wajen wassafa dabarun da za a bi don fita daga cikin wannan kangi da kasar ta fada tare da kawo hanyoyin da za su rage matsi da al’umma ke ciki.

Tsohon gwamnan na babban bankin Nijeriya ya yi kira ga masu hannu da shuni da su mika hannun tallafi ga masu karamin karfi don rage musu radadin wahalar da suke ciki.

Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su dukufa wajen yi wa kasar addu’ar ci gaba ba tare da duba da bambancin addini, kabila ko jam’iyyar siyasa ba

Ya kuma yi kira ga mutane jihar Kano da su kasance a kodayaushe masu da’a da girmama doka tare da kuma taimakekeniya tsakanin junansu

You may also like