Danna hoton sama domin kallon bidiyon
Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Baba
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna ne da Sheikh Muhammad Ahmad Baba wanda aka fi sani da As Sudani.
An haifi malamin ne a birnin Kaduna cikin 1976.
Ya fara karatunsa na makarantar allo tun a 1983, kafin ya shiga makarantar firamare ta ABS 1.
Malamin ya kammala makarantar Islamiyya matakin farko ne a 1990.
Ya samo sunan As Sudani ne daga Jami’atu Ifriqiyya al-Alamiyya ta ƙasar Sudan inda ya yi karatunsa na jami’a.
Ku kalli bidiyon domin ji daga bakin malamin.