Ku latsa sama don kallon bidiyon
Ku San Malamanku tare da Gwani Sagir Usman Madabo
An haifi Gwani Sagir Usman Madabo a unguwar Madabo cikin birnin Kano, kuma ya fara karatunsa ne a hannun wani Mallam Kyauta. Ya sauke Al-Qur’ani ne da ƙarfin gwiwar Khalifa Isyaku Rabi’u.
Ya halarci Adakawa Firamare, wadda ya kammala a shekarar 1985, kafin ya tafi sakandiren Gwammaja 2 wadda ya kammala a 1990.
Gwani Sagir Madabo ya kuma halarci kwalejin nazarin shari’a da addinin Musulunci ta Aminu Kano wato Legal kafin ya wuce zuwa Jami’ar Bayero inda ya karanta babbar difloma a fannin nazarin harkokin shari’a.
A yanzu haka, karatun digirinsa na biyu a Jami’atun Nahda da ke Jamhuriyar Nijar, inda yake fatan kammalawa a 2023.