Ku San Malamanku da Malam Ibrahim Mai Ashafa
Fitaccen malamin nan na jihar Kano Malam Ibrahim Kabiru wanda aka fi sani da Malam Ibrahim Mai Ashafa ya ce ba bu inda ya fi burge shi cikin littafin Ashafa kamar babin suffofin Annabi Alaihissalam.
Malamain wanda aka haifa a jihar Kano a 1976, ya ce ya tashi ne a gaban Sheik Aliyu Harazimi, ya ce babu wani waje a cikin littafin Ashafa da ba ya da daɗin karantawa.
Kamar dai mafi yawan malamai, shi ma Malam ya fara karatunsa ne a gaban iyayensa kafin daga bisani a kai shi karatu gaban malamai.
“Mun fara da karatun Alƙurani mai girama hannun Malam Bala, daga baya muka koma hannun Malam Baffa gidan Sarkin Tsakuwa, kuma a nan ne muka yi haddar Alƙur’anin”.
Malam ya yi karatun sakandirensa a Shahuci wato Aliya a shekarar 1988, kuma ya kammala a makarantar.
Ya ci gaba zuwa makarantar nazarin shari’a da addinin Musulunci ta Aminu Kano, Amma duk da haka Malam na gwamitsawa da karatun soro bai daina ba.
Mun yi karatu a hannun Malamai da dama
“Na yi karatu a wajen Malam Shu’aibu wani maƙocinmu, na yi karatun tarihi da hadithi a wajensa.
Akwai Malam Ahmad mutumin Kamaru na yi karatun littafan fiqhu a wajensa, irinsu Ishimayi da Ahalari da dai sauransu”.
Malam ya ce ya yi karatu a wajen Malam Muhammad na Ƙofar Na’isa, ga Malam Muhammadu Ƙani sai Shehu Malam Abdullahi Uwais da har yanzu ina karatu a wajensa.
Ina da mata biyu ɗaya ta rasu
“Ina da mata biyu ɗaya ta rasu, ‘ya’yana tara amma ɗaya ya rasu, yanzu akwai mata huɗu da maza huɗu”.
Ba zan taba mantwa da Shehu Aliyu Harazmi ba
Malam ya ce bai taɓa fita ko ina karatu ba, duka karatunsa ya yi shi ne a gida.
Abin da Maulana ya taɓa yi min da ba zan manta da shi ba, shi ne ranar da yace inzo mu tafi Saudiyya, da kuma ranar da ya bani kyautar gida.