Ku San Malamanku tare da Malam Usman Nagoda



Bayanan bidiyo,

Ku San Malamanku tare da Malam Usman Nagoda

A wannan mako, shirinmu na Ku San Malamanku ya tattauna da malamin addinin Musulunci Malam Usman Nagoda da ke birnin Kano.

An haifi malamin ne a birnin na Kano cikin 1977.

Ya fara karatun allo ne a wurin kakansa, Malam Danjuma Mai Tosaro.

Malamin ya ce daga nan ne ya shiga makarantar firamare ta Magwan, kuma bayan ya kammala ya tafi Sakandire a Kazaure.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like