Taɓa hoto na sama domin kallon bidiyon mai ƙunshe da tarihin malamin
Ku San Malamanku tare da Mallam Muhammad Sallah Jamil
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna ne da Mallam Muhammad Sallah Jamil.
An haifi malamin a garin Agaie da ke jihar Naija a shekarar 1974, inda ya yi karutan allo a gaban mahaifinsa wanda shi ma babban malami ne da yake bayar da karatu a gidansa.
Allah Ya azurta malamin da AlƘur’ani tun yana shekara wajen tara da haihuwa.
Bayan nan ya ce mahaifinsa ya sanya shi a makarantar Boko inda ya yi furare a nan garin nasu na Agaie, amma iya nan ya tsaya a karatun bai ci gaba ba.
Ya ci gaba da karatun littattafai a gaban mahaifin nasa, kuma bisa irin nasibi da Alla Ya yi masa a karatun, sai aka ware masa wani sashe a makarantar gidan nasu lokacin bai fi shekara 15 ya riƙa karantarwa.
Mallam ya ce ba abin da ya fi so kamar ya ga ana karatun AlƘur’ani ana zikirin Allah, kuma ana yi wa manzon Allah (SAW) salati.
Fannin da ya fi ƙwarewa a karatun addini shi ne Sufanci da lugga da kuma tafsirin AlƘur’ani.