Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdulƙadir Saleh Kazaure



A wannan makon filinmu na Ku San Malamanku ya tattauna da Sheikh Abdulƙadir Saleh Kazaure da ke garin Kazauren jihar Jigawa a Najeriya.

Malamin ya fara karantunsa na boko a Makarantar Kudu Firamare, kafin a kai shi karatun allo yana ɗan shekara bakwai a tsangayar Balbela cikin birnin Maiduguri.

Ya shiga Fitacciyar Sakandiren SAS ta Kano, kuma bayan ya kammala ne ya tafi Kwalejin Nazarin Shari’a da Al’amuran Addinin Musulunci ta LEGAL da ke Kano. Ya yi karatu a ƙarƙashin fitaccen malamin nan, Sheikh Jaafar Mahmud Adam. Ya kuma samu tallafin karatu a ƙarƙashin Cibiyar Al-Muntadah, sannan ya tafi Sudan inda ya kammala karatun digirinsa na 2 a shekara ta 2013.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like