Latsa hoton domin kallon bidiyon
Ku San Malamanku tare da Sheikh Haruna Sadi Alfindiqi
An haifi Sheikh Haruna Sadi Alfindiqi da aka fi sani da Baban Saddi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
Ya yi karatun Firamare a Makarantar Tudun Maɗatai daga shekarar 1981 zuwa 1987 daga nan kuma ya je makarantar Sakandare duk a jihar Kano.
Malamin addinin ya shaida wa filin Ku San Malamanku cewa ya yi akasarin karatunsa a gaban mahaifinsa, Malam Sadi Alfindiqi duk da cewa akwai makarantar da yake zuwa musamman ta dare.
A cewarsa, akwai malamai kamar Sheikh Malam Nasir Kabara da Sheikh Malam Yusuf Makwarari da Sheikh Malam Ibrahim Khalil da ya tasirantu da karatunsu.
Sheikh Haruna Sadi Alfindiqi ya ƙara da cewa an fi yi masa tambayoyin da suka shafi ɗariƙa sannan a ɓangaren Fiqhu, ana yawan yi masa tambayoyin da suka shafi mata kamar al’ada da nifasi da zamantakewa da kuma sallah.