Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Sani Abubakar
Sheikh Muhammad Sanusi Abubakar wanda aka haifa a unguwar Marmara da ke birnin Kano, ya fara karatun Al’qur’ani da fiqihu a garin Goundre da ke jamhuriyar Kamaru tun yana dan shekara hudu.
Ya kuma shiga makarantar Dandago Primary School a birnin Kano bayan komawarsa gida daga jamhuriyar Kamaru.
Ya je jami’ar International University ta Madina inda ya kammala a 1991 a fannin Shari’a.
“Duk a malaman da na amfana da iliminsu babu kamar babban yayana wato Sheikh Aminuddeen Abubakar.”
Sheikh Dr Muhammad Sanusi, shi ne limamin Masallacin Jumu’ah na Sheikh Zarban da ke ‘Yankaba a birnin Kano.