Wani dan Majalisar wakilai mai suna Timothy Golu yace ba shakka cewa aljanu sun samu shiga jikin tsohon shugaban kwamitin kasafi na majalisar,
Hon Jibrin. HonGolu yace sai ‘yan kasar nan sun taimaka da addu’a domin da alamu bakaken aljanu ne jikin sa, watau Hon Jibrin.
Hon. Jibrin Hon. Golu yana maida martini ga zargin da shi Hon. Jibrin yayi ga ‘Yan Majalisar, a cewar Hon. Jibrin, wanda tuni an dakatar da shi daga Majalisar, kowane dan majalisa yana tashi da Miliyan N20 a kowane wata na ayyukan bogi. Dan Majalisa Hon. Timothy Golu mai wakiltar Plateau, yace Hon. Jibrin din karya kurum yake zubawa ‘Yan Najeriya.
Hon. Golu dai dan Jam’iyyar PDP ne, yana wakiltar wani yanki na Jihar Plateau a Majalisar, yace Hon. Jibrin yana fama da iskokai ne a Jikin sa, don haka yana bukatar gudumuwar adda’a. Hon. Golu dai yace inda za a gane Hon. Jibrin karya yake yi, a baya yace Naira Miliyan 10 aka ba kowane dan majalisa, yanzu kuma ya dawo yace Miliyan 20, gobe ma zai canza. Dan majalisar na Jihar Plateau yace Jibrin na kokarin yi wa Dogara, wanda shine Shugaban Majalisar sharri ne kawai. Hon. Timothy Golu yace ‘yan majalisar kaf suna bayan Yakubu Dogara.
Golu yace Hon. Jibrin ya zama wani ala-ka-kai a Majalisar, ya kuma dace da aka dakatar da shi. Golu yace aikin Majalisa na gayya ne, ba haka nan ake yi ba. Hon. Jibrin ya na tunani don yana da kudi shikenan zai yi abin da ya ga dama, Inji dan majalisar. Golu yace yanzu babu mai ganin sa da mutunci.