Ku yiwa Yusuf  addu’ar samun sauki, gwamnan jihar Oyo ya shawarci yan Najeriya 


Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya shawarci yan Najeriya kan su yiwa iyalin shugaban kasa addu’a ba kakkautawa musamman ma akan Allah yabawa dan shugaban kasa  Yusuf lafiya.

Wannan kira na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan akan harkar sadarwa, Mista Yomi Layinka  ya rabawa manema labarai a Ibadan.

Yusuf wanda yayi hatsari a Abuja ranar Talata lokacin da yake tsaka da tsula a gudu akan babur.

Ajimobi ya bayyana hatsarin a matsayin wani abu marar daɗi mai karya zuciya inda yayi addu’ar Allah Subhanahu wata’ala zai bawa dan shugaban ƙasar lafiya.

“A,  al’adarmu ta yan Afirka ta lura da yan’uwanmu ina shawartar yan Najeriya da su cigaba da tunawa da iyalin shugaban kasar a cikin addu’o’insu musamman a cikin wannan mawuyacin halin da suke ciki.”

You may also like