Kudin Fansho na Naira Dubu 2,400 Ne Duk wata –  AAmbassador Bashir Wali


Tsohon jakadan Nijeriya a kasar Masar da Iran, Ambasada Umar Bashi Wali, a jiya Litinin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dube shi kan naira dubu biyu da dari hudu da yake karba duk wata a matsayin kudin fansho.
A yayin da yake zantawa da jaridar Daily Trust, Ambasada Wali ya kara da cewa ya dauki tsawon shekaru wajen yi wa kasa hidima, inda a shekarun baya ake biyansa naira dubu hamsin a matsayin fansho a duk wata.
Ya kara da cewa duk gyaran da aka yi a fannin kudin fansho kudin da ake biyansa yana nan a yadda yake maimakon a kara masa.
“Duk da cewa a matsayina na tsohon Ambasada wanda ya yi wa kasa aiki a tsawon shekaru 36, na kai tsawon shekaru takwas ina karbar naira 1,800 a duk wata a matsayin kudin fansho, daga baya aka kara zuwa 2,400.
“Yanzu na kai shekaru 82 kuma na tsufa. Na rubuta korafi da dama kan hakan zuwa ofishin kula da kudin fansho dake Abuja amma babu amsa. Kuma na je har ofishin da kaina domin mika korafi na kan lamarin. Inda suka yi alkawarin gyarawa amma har yanzu shiru. Don haka ina kira ga wadanda ke da alhaki kan lamarin da su taya ni yin duba kan lamarin”, inji Ambasada Bashir Wali.

You may also like