Fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari bai koma kasar kamar yadda aka tsara ba ne saboda likitansa ya bukaci ya zauna domin sake duba lafiyarsa.
Kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa bayan an gudanar da gwaji a kan shugaban kasar sau daya, an sake yin gwaji a kansa kuma sakamakon gwajin na biyu ake jira shi ya sa likitan ya bukaci Shugaba Buhari ya zauna har sai an fitar da sakamakon.
Sai dai ya ce yana fatan ba za a dauki dogon lokaci ba kafin a fitar da sakamakon gwajin na biyu.
Da BBC ta tambaye shi kan ko wacce rashin lafiya ce ke damun shugaban kasar, sai Mr Shehu ya ce, “Wannan sirri ne tsakanin maras laafiya da likitansa”.
Amma ya yi ira ga ‘yan Najeriya su yi wa shugaban kasar addu’a.
A ranar 19 ga watan Janairun 2017 ne dai shugaban ya ce zai tafi hutun ne ranar 23 ga watan Janairu sannan ya dawo ranar shida ga watan Fabrairu.