Kungiyar Jihadi ta Isis ta dau nauyin harin Nice, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 84 a ranar alhamis da ta gabata. A cikin wata takaitaciyar sanarwa da kungiyar TA Isil ta fitar a shafinta na Internet, ta danganta maharin da zama sojanta da ta ba umarni kai hari a kan daya daga cikin kasashen dake cikin rundunar hadakar dake yakar kungiyar a kasashen Syriya da Iraki. Sanarwar da yanzu haka mahukumtan Faransa ke kokarin tabbatar da sahihancinta.
A dai gefen kuma, Faransa ta kaddamar da zaman makoki na kwanaki 3, bayan faruwar harin ta’addancin Nice dake kudu maso gabashin kasar Faransa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 84 wadanda suka hada da yara 10, da wani matashi dan kasar Tunisiya ya hallaka a ranar da kasar ke bikin tunawa da zama jamhuriya a 1880.