
Yan sandan jihar Enugu na zargin yan kungiyoyin asiri (cultists) da kashe wani Ayaka da be wuce shekaru Ashirin (20),yan kungiyoyin Asirin sun harbe shi ne akan hanya daga bisani suka tsere kafin bayanar yansandan.
wayanda alamarin ya faru a gabansu su bayana wa majiyar labarai cewa harbin ya tsorata jama’an yankin da dama. su kara da cewa yan kungiyar Asirin kusan su goma ne suka zo yankin da motoci biyu tare da miyagon bindigogi sun kuma karbe wa wani mutumi motarsa akan hanyar su na tserewa.
Sun kara da ce bayan tafiyar ya kungiyoyin Asirin ,mutane suka fara fitowa daga shagonansu da gidajin su,su na zuwa wajen da alamarin ya faru,anan suka sami mutumin da yan kungiyar suka harba a mace a cikin kwata.
Wasu daga cikin mutanen su bayana cewa wanda aka kashe shima babane a wata kungiyar asirin yanki,me magana da yawon yansandan jihar Enugu,Ebere Amaraizu, ya bada tabacin cewa bayan faruwar Alamarin hukumarsu sun kashe daya daga cikin yan kungiyar Asirin kuma a yanzu haka sun kama muatne biyu daga cikin yan kungiyar bayan su yi musanyar wuta da yan kunjiyar Asirin.

