Kungiyar Boko Haram Ta Sako Yan Matan Chibok Su 82


​Kungiyar Boko Haram ta sako yan matan sakandiren Chibok 82, daga cikin yan mata 276 da sukayi garkuwa da su. 

Wata majiyar soja tace an samu nasarar sako yan matan ne bayan tattunawa tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da kuma kungiyar ta Boko Haram. 

Majiyar tace yan matan da aka saka suna can garin Banki dake iyakar Najeriya da Kamaru, kafin daga bisani a daukosu zuwa Maiduguri. 

Shugaban kasa Muhammad Buhari yasha nanata cewa, gwamnatinsa na iya bakin kokarinta don ganin an samu nasarar ceto yan matan. 

Yayin bikin cika shekaru uku da sace yan matan,Buhari ya shawarci yan Najeriya da kada su fidda ran cewa yan  mata baza su dawo gida ba. 

Yayi alkawarin dawo da yan matan ga iyayensu.

A ranar 14 ga watan Afirilun shekarar 2014 ne, aka sace yan matan su 276, daga makarantar sakandire dake garin Chibok lokacin da suke zana jarrabawar kammala sakandire.

You may also like