Kungiyar CAN Ta Tabbatar Da Cewa ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 57KADUNA, NIGERIA – Cikin ‘yan-kwanakin da su ka gabata dai hare-haren ‘yan-bindiga sun yi sauki a sassan Jihar Kaduna har ma gwamna Nasuru Ahmed El-Rufa’i na bada tabbacin ci gaba da walwalar al’umma saboda nasarorin da jami’an tsaro ke samu kan ‘yan-bindiga a wasu yankuna na Jihar. To sai dai shugaban kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN, reshen jahar Kaduna, Rabaren John Joseph Hayab ya ce har yanzu akwai saura rina a kaba game da matsalar tsaro.

Rabaren Hayab ya ce wasu mabiya na cikin ibada a yankin Kurmin Juwa dake karamar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, kawai sai ‘yan-bindiga su ka afka musu, inda su ka sace mutane 57, amma kuma mutane 14 sun samu tsira, yanzu saura mutane 43 a hannun ‘yan-bindigan, kuma har sun fara maganar kudin fansa.

‘Yan Bindiga

‘Yan Bindiga

Dama dai gwamna Nasuru Ahmed El-Rufa’i ya ce duk da nasarar da aka yi kan ‘yan-bindigan wasu sun sauya mafaka, ko da ya ke dai gwamnan ya ce ko ina ‘yan-bindigan su ka shiga ma, za a gama da su.

Masani kan harkokin tsaro Manjo Muhammadu Bashir Shu’aibu Galma mai ritaya ya ce dama duk dabi’ar ‘yan-bindiga ce su rinka kai hare-haren don nuna gazawar gwamnati.

Manjo Galma ya ce yanzu ya ragewa jami’an tsaron ne su maida hankali wajen ganin sun farwa ‘yan-bindigan a sabbin guraren da su ka fara kai hare-haren baki daya.

Kimanin wata guda kenan da samun saukin hare-haren ‘yan-bindiga a Jihar Kaduna sakamakon sauya salon aikin jami’an tsaro ta yadda su ka fara bin ‘yan-bindiga har daji su na murkushe su, amma hare-haren kwananan a yankin kudancin Kaduna da kuma Birnin Gwari na neman maida hannun agogo baya.

Saurari cikakken rahoton daga Isah Lawal Ikara:

You may also like