Rahotanni sun nuna zanga-zangar da kungiyar daliban Nijeriya NANS ta yi a shekaranjiya Alhamis ta nuna rashin jin dadin su ga rikicin kyamar bakin da ake yi a Afrika ta kudu wanda ya kai ga jikkata ‘yan Nijeriya, da gidajensu har da dukiyoyin su.
Kungiyar Daliban ta baiwa kamfanonin kasar Africa ta Kudu da ke Najeriya kwanaki biyu su tattara kayansu don barin kasar, kamfonin da suka dade suna cin kasuwa a Nijeriya kaman su MTN, DSTV da Shoprite.
Shugaban daliban, Haruna Kadiri a wata hira da ya yi da manema labarai a ofishin DSTV a Abuja ya ce ‘yan kasar Afrika ta kudu sun dade suna haka kuma idan basu bari ba ‘yan Nijeriya za su yi ramuwar gaya kan Kamfanonin su da ke Nijeriya.
Ya ce suna bukatar ofishin jakandancin Najeriya ya dauki matakin kawo karshen wannan matsala domin samun kwanciyar hankalin ‘yan kasar a Africa ta Kudun