Kungiyar Fulani Ta Kasa Zata Shigar Da Gwamnatin Jihar Taraba Kara A Kotun Manyan Laifuka Ta DuniyaKungiyar Fulani Ta kasa na zargin cewa akwai sa hannun gwamnatin jihar taraba wajen kisan gillar da akayiwa fulani a garin mambila dake karamar hukumar Sardauna dake jihar ta taraba. 
Alkaluman daba na gwamnati ba sun nuna cewa sama mutane dubu daya da dabbobi dubu uku mambilawa suka kashe a garin na mambila. 
Saboda hakane kungiyar fulani da kasar Najeriya tace zata shigar da kara a babban kotun manyan laifukan ta’addanci ta duniya domin a bi musu hakkin barnar da akayi musu. 

You may also like