Kungiyar Hadin Kan ‘Yan Arewacin Najeriya A Amurka Ta Zabi Matasa Zalla A Matsayin ShugabannintaAn kuma cimma matsaya a taron da aka gudanar na kwanaki uku, da neman hanyoyi, da kuma daukar sababbin matakan cimma burin kungiyar na inganta rayuwar ‘yan arewacin Najeriya da ke zaune a Amurka.

Babban bako kuma a wurin taron, Mai Martaba Sarkin Machina da ke jihar Yobe, Dr Bashir Albishir Bukar, ya yaba irin hadin kan dake tsakanin membobin kungiyar ba tare da nuna banbancin addini ko kabila ba. Bisa ga cewarshi sha’awar ganin yadda ‘yan kungiyar su ke kyakkyawar mu’amala da juna ya sa a ko da yaushe ya ke jin dadin halartar tarukan kuniyar, ya kuma ce ya kamata sauran ‘yan Najeriya musamman ‘yan arewacin kasar su yi koyi da kungiyar.

Basaraken ya kuma yi kira ga membobin kungiyar su karfafa irin wannan zamantakewar tsakanin al’umma a yankunan da su ka fito a Najeriya domin ganin an sami zaman lafiya da fahimtar juna kamar yadda ake yi a kungiyar.

Mai Martaba Sarkin Machina a jihar Yobe, Dr Bashir Albishir Bukar

Mai Martaba Sarkin Machina a jihar Yobe, Dr Bashir Albishir Bukar

A hirar shi da Muryar Amurka, shugaban kungiyar zumunta mai barin gado Philip Moses ya bayyana nasarorin da kungiyar ta cimma a cikin shekaru biyar da suka shige karkashin shugabancin sa da kuma hanyoyin da kungiyar za ta ci gaba da taimakawa al’umma.

Bisa ga bayaninsa, kungiyar ta ba kungiyoyi masu zaman kansu da dama tallafin Naira dubu dari biyar kowannensu domin ci gaba da gudanar da ayyukansu na tallafawa al’umma, a jihohi dabam dabam na arewacin Najeriya da kuma babban birnin tarayyar Abuja .

Sauran ayyukan da kungiyar ta gudanar kuma sun hada da gina rijiyar burtsatsai a jihar Nassarawa, da kuma gyara azuzuwan makarantar firamare, da samar da kayan ilimantarwa a jihar Kaduna. Kungiyar ta kuma gudanar da wadansu ayyukan kula da lafiya, da tallafawa al’umma da kayan masarufi a lokacin da aka fuskanci kalubalen rayuwa sakamakon barkewar annobar Korona, da dai sauransu.

Wadansu membobin Kungiyar Zumunta

Wadansu membobin Kungiyar Zumunta

Shi ma a nasa bayanin Dr Mohammed Ladan wanda ya yi shugabancin kungiyar Zumunta tsakanin shekara ta dubu biyu da uku zuwa dubu biyu da bakwai, ya bayyana dalilin kafa kungiyar da kuma inda ya kamata kungiyar ta bada karfi nan gaba.

Ya ce an kafa kungiyar Zumunta ne da nufin taimakon ‘yan arewacin Najeriya mazauna Amurka musamman wadanda suka zo baki da iyalansu da ke da bukatar hanyar rayuwa ta yau da kullum, da taimakawa ‘ya’yan membobin kungiyar da kudin biyan makarantun jami’a.

Ya ce duk da ci gaban da aka samu a kungiyar, wani abinda ya kamata a maida hankali a kai shi ne koyawa yaran membobin al’adun Najeriya.

Babban taron Kungiyar Zumunta na kasa

Babban taron Kungiyar Zumunta na kasa

Taron ya sami halarta membobin kungiyar daga dukan jihohin Amurka da kuma manyan baki daga Najeriya.

An kamala taron na bana mai taken sake saduwar dangi, sake lalle, da kuma ci gaba, tare da zaben sababbin shugabannin kungiyar da suka hada da Sunday Bitrus tsohon sakataren kungiyar na kasa a matsayin sabon shugaba, da kuma Rhoda Runi Embu a matsayin mataimakiyar shugaba wadda kuma ta kasance mataimakiyar shugabar kungiyar mace ta farko. A wannan shekarar kuma a karon farko mace ta tsaya takarar shugabar kungiyar.

Sababbin Shugabannin Kungiyar Zumunta

Sababbin Shugabannin Kungiyar Zumunta

A wannan karon, galibin shugabannin kungiyar da aka zaba matasa ne, da suka hada da Faud Khaleel da aka zaba a matsayin babban magatakardan kungiyar, wanda aka haifa bayan an kafa kungiyar aka kuma rika zuwa da shi tarukan Zumunta tun yana dan karamin yaro, har ya girma ya zama daya daga shugabannin matasa kafin zabensa a matsayin daya daga cikin shugabannin kungiyar na kasa, abinda aka zayyana a matsayin daya daga cikin nasarorin kungiyar da ya nuna tabbacin dorewarta.

A jawabinsa bayan zabe, sabon shugaban kungiyar Sunday Bitrus, ya yi alkawarin dorawa a kan nasarorin da magabatansa suka cimma, da kuma gabatar da sabbin hanyoyin cimma gurorin kungiyar.

A matsayinshi na matashi, ya ce za su yi aiki tare da matasa a Najeriya domin ganin yadda za su iya hada hannu su shawo kan matsalolin da suka addabi yankin arewacin kasar.

Za a gudanar da taron kungiyar shekara mai zuwa a Washington DC fadar mulkin gwamnatin Amurka.

An kafa kungiyar zumunta shekaru talatin da suka shige karkashin jagorancin Aliyu Mustapha Sokoto, shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka yanzu, a matsayin shugaban kungiyar na kasa na farko.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

You may also like