Kungiyar IPOB Zata Kaddamar Da Gidan Rediyon Hausa



Kungiyar nan mai Fafitkar kafa kasar Biyafara ta IPOB ta bayyana cewa a ranar Asabat mai zuwa ne za a kaddamar da sabon gidan rediyo wanda zai rika gudanar da shirye shiryensa a cikin harshen Hausa.

Kakakin Kungiyar, Emma Powerful ya ce manufar kafa gidan Rediyon shi ne na wayar da kan ‘yan Arewa tare da ingiza tawaye kan masu cin zarafin ‘ya’yan kungiyar inda ya nuna cewa da zarar an kaddamar da Rediyon mai suna “Radio Nigeria Hausa service”, zai rika gudanar da shirye shiryensa da misalin Karfe bakwai na Yamma.

You may also like