
Asalin hoton, AFP
Kungiyar IS wadda ta yi wannan ikirarin a madadin reshenta na lardin Afrika ta yamma wato ISWAP, sun yi iƙirarin kai harin ne a ranar Litinin a kan wata majami’a ko Coci da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi, inda mutum biyu suka mutu, wadanda kungiyar ta ce masu gadi ne.
Cikin sanarwar tata, kungiyar IS din ta bayyana cewa maharan sun yi amfani ne da bindigogi masu sarrafa kan su.
A cewar sanarwar, bayan kisan mutum biyun ne sai sauran mutanen da ke wajen suka watse, kowa ya yi ta kan sa.
Sai dai kungiyar ba ta yi cikakken bayani ko maharan sun samu damar kutsawa cikin cocin ba.
Wannan dai a cewar kungiyar, shi ne hari na 15 da reshenta, wato kungiyar ISWAP ta kai a jihar Kogi a cikin shekarar da ta wuce, wato 2022.
Har yanzu babu wani bayani daga jami`an tsaro ko mahukunta a Najeriya game da wannan harin na ranar Litinin.
Kazalika mafi yawan kafofin yada labaran Najeriya ba su ba da labarin harin ba.
Kungiyar ISWAP dai ta yi fama da rikicin cikin gida a baya-bayan nan, da ya kashe mata kaifin kai hare-hare inda har ta kai ga suna far wa juna da bangaren magoya bayan Shekau.
Haka kuma rikicin ne ma ya yi sanadin mutuwa ta kunar-bakin-wake da jagoran Boko Haram din wato Abubakar Shekau ya yi.