Kungiyar ISIS ta tabbatar da mutuwar shugabanta Abubakar Al-Baghdadi a rahoton da wasu kafafen yada labarai suka bayar a yau Talata.
A cewar mai gabatar da labarai tashar talabijin ta Al-Sumaria,Al-Baghdadi ya mutu kuma za a sanar da wanda zai gaje shi nan ba dadewa ba.
A ranar 16 ga watan Yuni ne ma’aikatar tsaron kasar Rasha tafitar da wata sanarwa inda tace akwai yiyuwar sojin samanta sun kashe Al-Baghdadi a wani hari da suka kai a wajen birnin Raqqa a karshen watan Yuni.
Ma’aikatar tace tana kokarin tabbatar da mutuwarsa ta hanyoyi daban-daban.
Al-Baghdadi ya fara bayyana ne a shekarar 2014 lokacin da ya sanar da kafa kasar daular musulunci a yankin gabas ta tsakiya mai hedikawata a birnin Mosul na kasar Iraqi.
Tun wancan lokacin kafafen yada labarai da dama sun sha bada rahoton mutuwarsa, amma babu rahoton da ya tabbatar da haka.
A jiya ne dai gwamnatin kasar Iraqi ta tabbatar da kwace birnin Mosul daga yan kungiyar ta ISIS.