Kungiyar Izala Na Taya Daukacin Musulman Duniya Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci (1438).


Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil bid’ah wa’iqamatis Sunnah ta kasar Nijeriya Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, a madadin kungiyar yana taya Al’ummar Musulmi murnar shiga sabuwar Shekara ta Musulunci, Shugaban ya kuma yi addu’a Madaukaki ya wadatar da mu ya kuma karba mana.
Shugaba Sheik Abdullahi Bala Lau ya kara da kira ga mutane da su waiwayi baya su duba abinda suka aikata na kuskure su nemi gafarar Allah Madaukaki, saboda a koda yaushe ana bukatar bawa ya rika tunanin abinda ya aikata cikin kwanuka da suka shude, Sannan Shugaban ya roki Allah kan dacewa a cikin wannan sabuwar Shekara ta Musulunci.
Sheik Lau ya kuma yi kira ga Musulmin da suke yin Azumi don murnar shiga sabuwar shekara da su nesanci aikata haka din domin kirkirarren abu ne a Musulunci wanda Annabi mai tsira da aminci da Sahabbansa masu daraja da tabi’ai ba su aikata haka ba, don haka Shugaban yake kira da mu kara lazimtar Sunnar Annabi mai tsira da aminci a kowane yanayi naa ibada ko mu’amala.
Haka zalika Baya daga cikin sunnah musayar sakonni ko shirya bukukuwa a dalilin sabuwar shekarar, lokaci ne da yakamata mutum ya yi kuka gami da zub da hawaye sakamakon an gabtare wani gibi na kwanakinsa na duniya. Sannan ya yi takaicin asarar lokutansa da ya yi a shekarar da ta shude, cikin shirme da sharholiya marar amfani, sannan ya yi kokarin daura damarar cike wadancan gurbi da kyawawan aiyuka cikin sabuwar shekara.
Muna addu’ar Allah ya gafatar mana kura-kuren da muka yi a wancan shekara! Ya sanya wannan sabuwar shekara ta zama shekarar kwanciyar hankali a kasashen musulmai, da yawaitar arziki, da ci gaba gaba da yaduwar Musulunci. Amin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like