Kungiyar JOHESU, ta ci alwashin cigaba da yajin aiki


Gamayyar kungiyoyin ma’aiktan kiwon lafiya da ake kira JOHESU sun ci alwashin cigaba da yajin aikin da suke a fadin kasa baki daya.Har sai gwamnatin tarayya ta aiwatar alkawarin da suka cimma a tsakaninsu ranar 30 ga watan Satumba na shekarar 2017.

Kungiyar ta JOHESU ta bayyana hak wurin wata zangar-zangar lumana da sakatariyar uwar kungiyar ta kasa ta shirya a Abuja.

Shugaban kungiyar na kasa, Josiah Biobelemoye,ya ce an shirya taron gangamin ne domin sanar da yayan kungiyar cigaban da aka samu ciki har da umarni da kotu ta bawa yayan kungiyar na su koma bakin aiki.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, ya rawaito cewa kotun dake sauraran karar ma’aikata ta bayar da umarni ranar 25 ga watan Mayu,dake cewa yayan kungiyar su koma bakin aikinsu ba tare da bata lokaci ba.

Biobelemoye, ya ce kungiyar tana da damar bijirewa ko kuma bin umarnin kotun.

Ya lura cewa tun bayan da kungiyar ta tsunduma yajin aiki ranar 18 ga watan Afirilu, sau takwas suka zauna tattaunawa da wakilan gwamnati.

You may also like