Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam A Nijeriya Ta Bukaci Amurka Da Ta Sanya Kungiyar Shi’a a Jerin Kungiyoyin Ta’addanci


 

 

Kungiyar lauyoyin da ke rajin kare hakkin dan Adam a Nijeriya sun aika takardar korafi ga ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya game da ‘yan shi’a da ayyukansu a kasar.

Kungiyar ta ce ‘yan Shi’a na yi wa tsaron Nijeriya da ilahirin kasashen yammacin Afirka barazana.

Haka kuma ta aika takardar ga ofishin jakadancin kasar Jamus da na Majalisar Dinkin Duniya da ke babban birnin tarayya Abuja.

Wasikar koken wacce daraktan bincike na kungiyar ya sanyawa hannu ta bayyana kungiyar da Ibrahim El-zakzaky ke yi wa jagoranci a matsayin ‘yan tawayen da Iraniyawa ke mara wa baya.

Wannan dai na zuwa kwanaki 2 kawai bayan da gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya zargi ‘yan shi’an da abu makamancin wannan.

El-Rufa’i ya bayyana cewa su ‘yan shi’a ba su bin dokokin kasa da kuma shugabannin Nijeriya, kuma yunkurinsu kawai shi ne su yi karfin da za su iya ta da hankali jama’a.

Dama dai a ‘yan kwanakin baya, Amurka ta fito karara ta nuna rashin jin dadinta dangane da yadda jami’an tsaron Nijeriya ke yi wa kungiyar dirar mikiya.

A wasikar, Kungiyar ta janyo hankalin Amurka da cewa, a maimakon afkawa ‘yan kungiyar ta Shi’a da ake yi, su ‘yan Shi’an ne ke afkawa ‘yan Nijeriya saboda basa bin dokokin kasa.

Sannan kungiyar lauyoyin ta yi kira ga gwamnatin Amurka da ta saka Islamic Movement of Nigeria (Kungiyar Shi’a) cikin ayarin kungiyoyin ‘yan ta’ada na duniya.

You may also like