Kungiyar Kasashen Larabawa ta taya Trump murna


582d42585105a

 

Kungiyar Kasashen Larabawa ta aike da sakon taya murna ga sabon zababben shugaban kasar AMurka Donald Trump.

A sakon da Kungiyar ta aike, Sakatare Janar din ta Ahmad Abu Gayt ya ce, suna taya Donald Trump Murnar nasarar lashe zaben shugaban kasa inda ya tunadar da irin dangantakar da ke tsakanin kasashen Larabawa da kuma Amurka.

A sakon nasu, an ja hankali game da yadda ba a bin hanyoıyi na adalci wajen yunkurin warware rikicin Falasdin da Isra’ila, inda suke fatan gwamnatin Trump za ta samar da manufofi masu kyau game da kasashen Gabas ta Tsakiya.

You may also like