Kungiyar Kasashen Musulmi za ta taimakawa wadanda ta’addancin Boko Haram ya shafa a Najeriya


 

 

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ta yi nazari game da yadda rikicin Boko Haram ya illata mutane a arewa maso-gabashin Najeriya inda za ta nemo hanyoyin taimaka musus cikin gaggawa.

Sanarwar da Daraktar Yada Labarai ta Kungiyar Misi Maha Akeel ta fitar ta bayyana cewa, Mataimakin Sakatare Janar na Kungiyar Jakada Hameed Opeloyeru ne ya sanar da shirin taimakon a yayin wata ziyarar aiki da ya kai zuwa Najeriya.

Sanarwar ta ce, manufar ziyarar ita ce a yi nazari tare da duba irin mawuyacin halin da jama’ar da ta’addancin Boko Haram ya shafa da kuma nemo hanyoyin taiaka muşu cikin gaggawa.

Opleru ya kuma ce, ziyarar wani bangare ce na irin aiyukan da suka yi alkawarinywa Najeriya a lokacinda shugaba Buhari ya gana da Sakatare Janar na Kungiyar Iyad Ameen Madani a birnin jeddah na Saudiyya a ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2015.

Bankin Cigaban Kasashen Musulmi IDB ya sanar da fara aiyukan koyarwa nah adin gwiwa a jihohi 9 na Najeriya wadanda sukahada da na Arewa maso-gabashin kasar.

You may also like