Kungiyar Kiristoci Ta Nemi Buhari Daya Cire Najeriya Daga Kungiyoyin Musulunci Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta kalubalanci Shugaban Kasa, Muhammad Buhari kan ya cire Nijeriya daga cikin duk wata Kungiya ta kasa da kasa wadda ke da alaka da Musulunci.
Kungiyar ta nuna cewa tsarin mulkin Nijeriya ya tabbatar da cewa bai kamata gwamnati ta rungumi wani addini a matsayin na kasa ba don haka kungiyar ta nemi Buhari ya fara cire Nijeriya daga kungiyar nan ta ‘International Islamic Liquidity Management Corporation (IILMC)’ wadda Nijeriya ke cikin ‘ya’yanta kuma aka nada Shugaban Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele a matsayin Shugabanta a taron da kungiyar ta yi a kasar Indonesiya kwanan nan.

You may also like