Kungiyar Kwadago Sun Janye Yajin Aikin Da Sukeyi a Jihar Zamfara A daren jiya Lahadi hadin guiwar kungiyoyin kwadago na NLC, TUC, NULGE, da NUT reshen jihar Zamfara, suka aminta suka jaye yajin aikin da suke yi bisa ga yarjejeniyar idan har gwamnati ta saba alkawari to za su koma bayan sati hudu. 

Shi dai yajin aikin an kwashe kwanaki 14 ana yin sa ba tare da jin bangaren gwanati ba, hasali ma har aka yi yajin aikin aka gama gwamna Abdulaziz Yari ba ya cikin jihar ta Zamfara. 

Su dai ‘yan kwadagon sun janye yajin aikin ne bisa ga kiraye-kirayen da dattijan jihar suka yi masu akan su jaye su ba su dama domin shiga tsakani domin su tattauna da gwamnati domin samun sulhu. 

Yanzu dai ido ya koma akan matakin da Gwamna zai dauka a yayin da ake dakun isowarsa yau a jihar.

You may also like