Kungiyar Ma’aikatan Mai Ta NUPENG Zata Fara Yajin Aiki



Kungiyar ma’aikatan mai wato NUPENG ta sanya ranar 9 ga watan Janairu a matsayin ranar da za ta fara yajin aikin kwanaki uku don nuna rashin jin dadin yadda kamfanonin mai na kasashen waje ke cin zarafin ma’aikatansu ‘yan asalin Nijeriya.
Shugaban Kungiyar na shiyyar Kudu maso Yamma, Alhaji Tokunbo ne ya sanar da haka a Legas inda ya nuna cewa sun bi duk matakan da suka dace na yin sulhu amma al’amarin ya gagara a bangaren kamfanonin. 

Ya kara da cewa sun nemi gwamnati ta shigo don ganin an kauce gudanar da yajin aiki yana mai cewa kamfanonin ba su biyan hakkokin ma’aikatansu da suka yi ritaya sabanin yadda suke kula da ma’aikatansu na wasu kasashe.

You may also like