Kungiyar Malaman Makaranta a Kaduna ta Janye Yajin Aiki


Aƙarshe Ƙungiyar Malamai ta Kasa NUT reshen jihar Kaduna ta janye yajin aikin sai baba ta gani da ta shiga ranar 8 ga watan Janairu kan korar kusan malaman makaranta 22000 da gwamnatin jihar tayi.

Malaman sun tsunduma yajin aikin ne domin nuna damuwarsu kan korar malamai 21,789 waɗanda aka ce sun fadi jarrabawar yan firamare dake aji uku da aka yi musu domin gwajin kwarewarsu.

Yajin aikin na kwanaki 10 ya jawo tsayawar harkokin karatu cak a makarantun gwamnati na firamare da kuma sakandare dake jihar.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun haɗin gwiwa na shugaban kungiyar, Audu T Amba ta NUT da kuma mataimakin sakataren Ƙungiyar Ango Adamu ta ce  a cimma matakin janye yajin aikin bayan wani taro da kungiyar ta gudanar domin duba halin da ake ciki musamman bayan furucin da gwamnatin jihar tayi bayan wani taro da sakatarorin ilimi 23 dake jihar.

Gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai ya sanar da bawa malaman dama a karo na biyu inda ya yi kira a gare su da su sake neman aiki a hukumar SUBEB ta jihar.

Ya yin da kungiyar ta NUT reshen jihar ta yaba da matakin da gwamnan ya ɗauka ta tabbatar masa da kara kwazo wurin gudanar da aikinsu.

You may also like