Kungiyar MASSOB Tayi Kira Ga Yan Kabilar Igbo Mazauna Arewa Da Su Fara Mayar Da Iyalansu Gida 


Kungiyar fafutukar tabbatar da kasar Biafra ta MASSOB ta bayyana watan Agustan wannan shekara a matsayin watan da dubban yan kabilar Igbo dake zaune a yankin arewacin kasarnan zasu koma gida. 

A wata sanarwa da aka fitar a Awka babban birnin jihar Anambra, Samuel Edesonu mai magana da yawun kungiyar yace an cimma wannan matsaya ne a taron shugabannin kungiyar na kasa da shugaban kungiyar Uchenna Madu ya jagoranta. 

Kungiyar matasan Arewa ne suka bawa yan kabilar Igbo dake zaune a yankin arewacin kasarnan wa’adin ranar daya ga watan Oktoban wannan shekarar kan su fice daga yankin.

Amma MASSOB ta shawarci yan kabilar ta Igbo da su fara komawa gida cikin watan Agusta domin muhimancin watan a tsarin kalandar Igbo. 

Yayin da suke kira ga matan Igbo kan su janyo hankalin mazajensu da yayansu wajen barin yankin kungiyar ta kuma yi kira ga shugabannin al’ummar Igbo dake jihohin arewa 19 dasu rubuta sunan duk wani dan kabilar ta Igbo dake zaune a yankin.

    


Like it? Share with your friends!

0

You may also like