Kungiyar Masu Motoci ta Kasa Sun Shirya Kai Hukumar Kwastam Kara Gaban Kotu.


 

 

Kungiyar wadanda suka mallaki motoci ta kasa wato, “Vehicles owners Association of Nigeria (VOAN)”a turance sun nuna rashin goyon bayansu, kan wa’adin da hukumar hana fasa kauri ta kasa wato kwastam, ta bawa masu motocin da aka shigo dasu ba bisa ka’ida ba da suje ofishin hukumar su biya musu haraji, daga ranar 13 ga watan maris zuwa 12 ga watan Afirilu, kin yin hakan kan iya jawowa a kwace motar mutum.

kungiyar ta bayyana matakin a matsayin abinda bazai yiwuba, inda  tayi barazanar zuwa kotu, matukar hukumar bata janye wannnan mataki ba cikin mako guda.

A wata wasika da kungiyar ta aikewa da shugaban hukumar, kanal Hameed Ali (mai ritaya) ta hannun lauyanta Tolu Babaleye. tayi kira ga hukumar ta kwastam da ta duba halin da yan Najeriya mutum miliyan 35 zasu shiga, matukar aka aiwatar da dokar.

You may also like