Kungiyar mata ‘yan jaridu na kasa (NAWOJ) ta nuna goyon bayan ta ga mukamin da aka baiwa Hajiya Hindatu Umar a matsayin shugaban karamar hukumar Argungu dake jihar Kebbi.
Shugabar kungiyar mata ‘yan jaridun reshen jihar Kebbi, Hajiya Maryam Atto Muhammad ce ta bayyana hakan a yayin da ta jagoranci membobin kungiyar a ziyarar da suka kaiwa shugabar karamar hukumar ta Argungu.
Hajiya Maryam, wacce mataimakiyarta, Misis Na’omi Paul Manga ta wakilce ta, ta bayyaba mukamin da aka baiwa Hindatu a matsayin wata hanya ce ta baiwa mata damar ganin an dama da su a gwamnati. Ta kuma ja hankalin matashiyar da ta kasance mai jajircewa kan gaskiya da rikon amana domin hakan zai taimaka wajen baiwa mata damar shiga cikin gwamnati.
Membobin kungiyar ta NAWOJ sun kuma yi wa Hajiya Hindatu fatan alkairi tare da addu’ar samun nasara a shugabancin nata.
A yayin da take mayar da martani, Hindatu ta nuna farin cikinta da ziyarar da kungiyar mata ‘yan jaridun suka kawo mata, sannan kuma ta bayyana musu cewa za ta dinga neman shawarar su a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Hindatu ta kuma yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga al’ummar Argungu domin ba ta hadin kai don ganin a ciyar da yankin gaba.