Kungiyar Matan Gwamnonin Arewa Sun Kaiwa Aisha Buhari Ziyara



Kawo yanzu, sama da mutane 6000 ne suka amfana da koyarwan iya dogaro da kai, karkashin shirin uwargidan shugaban kasa “Future Assured”. 
Wannan yana bayyana ne yayin da kungiyar matan gwamnonin Arewa (NWGF) suka kai wa uwargidan shugaban kasan Nijeriya Aisha Buhari.
Aisha Buhari, yayin da take tarbar bakin nata tace a kalla an kashe kudi naira miliyan biyu saboda horas da mutane 300 zuwa 400. Tace horaswan na dogaro da kai ya gudana ne a jihar Katsina da Lagos, yayin da yanzu haka kuma yake gudana a jihar Kano. Sannan kuma tace koyarwan zai gudana a sauran jihohi.
Sannan Uwargidan shugaban kasan ta godewa kungiyar da ta kawo mata ziyara.
Tun farko a nata jawaban, shugaban kungiyar Asma’u AbdulAzeez Yari tace wanann ne karo na farko da aka gabatar da ganawar a wannan shekara. Tace ganawar ta ta’allaka ne kan matsaloli dake bukatan shawo kan su cikin gaggawa.
Daga ciki, a cewar ta, hadda yanda za’ayi a shawo kan shaye shaye a arewacin kasar.

You may also like