Kungiyar Matasan Kiristoci Ta Najeriya (CAN)  Sun Nemi A Tsige El-Rufai. 



Kungiyar Matasan Kiristoci ta kasa sun yi kira da a tsige Gwamna Nasiru El-Rufai daga mukamin gwamnan jihar Kaduna. Sakamakon hirar da ya yi na cewa yana biyan Fulani makiyaya akan su daina kaddamar da farmaki ga ‘yan Kudancin jihar Kaduna. 
“Majalisar dokokin jihar Kaduna ya kamata ta gaggauta tsige El-Rufai saboda hada kai da ‘yan ta’adda suna kashe ‘yan Najeriya “. Kamar yadda shugaban kungiyar Injiniya Daniel David Kadzai ta fada.

You may also like