Kungiyar Shi’a sun nuna rashin gamsuwa da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na nunawa duniya Shugaban Kungiyar, Malam Ibrahim El Zakzaky bayan an rika yayata jita- jitar mutuwarsa a hannun jami’an tsaro.
Kakakin Kungiyar, Ibrahim Musa ya ce matakin gwamnatin ya saba hukuncin Babban kotun tarayya wadda ta nemi a saki El Zakzaky tare da biyansa diyya inda ya nuna cewa an yi kwaskwarima a faifan bidiyon da aka nuna El Zakzaky na bayani a takaice.